• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

IPAC Tayi Allah Wadai Da Kalaman Batanci Da Yan Siyasa Ke Yiwa Juna A Kano

BySani Magaji Garko

Feb 21, 2025

Kungiyar shugabannin jam’iyun siyasa ta kasa reshen jihar Kano (Inter Party Advisory Council IPAC) ta yi Allah-wadai da kalaman Batanci da wasu ‘yan siyasa ke yiwa juna a gidajen Rediyo da kafafen sada zumunta na zamani wato Soshiyal Midiya a jihar Kano.

Shugaban kungiyar kuma shugaban jam’iyar ZLP Isa Nuhu Isa ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a nan Kano da yammacin Alhamis.

Isa Nuhu wanda aka fi sani da Danfulani ya ce kalaman Batancin ya sabawa koyarwar addinin musulunci da dumokuradiyya da ‘yancin fadin albarkacin baki da duk wata ka’ida ta rayuwar dan Adam.

KU KARANTA: Ko A Dena Kashe Mutane A Gangamin Yakin Neman Zabe Ko Mu Hana Zaben — IPAC

“Ita siyasa shine idan wani yayi Mulki ya gama ko wani yana rike da Mulki yana yin abin da ba dai-dai ba a fito a fada, a fadi cewa manufofinsa ba dai-dai ba ne ko ayyukan da ya gabatar sun sabawa bukatun al’umma ko kuma aikin da yake kokarin yi ba shi al’umma suke bukata ba, maimakon a zo a kalli suffar da Allah yayi wa wani a kushe ko a yi kalaman Batanci ga reshi ko Danginsa ko kabilar da ya fito ko gida ko kalar fata ba,” inji Isa.

“Wani ya kushe kabila ko siffa mutum haramun ne a dumokuradiyya, haramun ne a musulunci, haramun ne a dabi’ance kuma ba dai-dai ba ne kuma baza mu zuba ido a cigaba da yin hakan ba,” inji shugaban.

“Mun fuskaci Siyasar Kano ta dauki wani salo na cin zarafi, na raina mutane, na Batanci, na lalata jihar Kano da tarbiyar da aka sammu da ita, na bata addinin musulunci don ba’asan musulmi da irin wadannan kalamai ba. Saboda haka muna jan hankali da su shugabanni masu yin wadannan kalamai da ma magoya bayansu, su tuna zasu koma su tarar da Allah, kuma mai zaka fada a matsayin hujja na cin mutuncin musulmi Dan uwanka?… Kai kasan makomar ka,” Inji Danfulani.

Ya ce masu yin wadannan kalamai su sani cewa ‘ya’yan da ‘ya’yan Yan uwansu da kuma zuriyarsu suke barwa abin fada. Yana mai cewa dukkanin bangarorin da suke kalaman Batancin ‘yan kungiyar IPAC ne saboda haka zasu dauki mataki na gani an kawo karshen matsalar.

KU KARANTA: Zaben 2023: Masu Yi Wa ƙasa hidima Ne Za Su Yi Aiki da BVAS – Shugaban INEC

Isa Nuhu Isa ya kuma zargi ‘yan Jaridu musamman masu shirye-shiryen siyasa da su bada goyon bayan ga cigaba da aikata kalaman Batancin inda ya ce da basu bawa Yan Siyasar dama ba da halin da ake ciki ba’a tsinci kai hakan ba.

Hakazalika shugaban ya kuma zargi jami’an tsaro da gaza daukar matakan da suka da ce domin hukunta masu yin kalaman Batancin ya na mai cewa da ana hukunci akan da wani da ya aikata lefin da abubuwa basu lalace ba.

Isa Nuhu Isa ya kuma ce kungiyar zata Bullo da tsare-tsaren da suka kamata na kawo karshen matsalar ciki harda ziyartar jami’an tsaro musamman rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano da hukumar tsaro ta farin kaya DSS da hukumar tsaro da kare dukiyoyin al’umma wato ‘Civil Defense’ da dukkan bangarorin da abin ya shafa domin kawo karshen matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *