Jam’iyyar NNPP ta Kasa reshen jihar Kano ta dakatar da wasu manyan mambobi hudu da suka hada da Sanata Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini da Sani Abdullahi Rogo da kuma Kabiru Alhassa Rurum, bisa zargin yiwa jam’iyyar Zagon Kasa.
Shugaban jam’iyyar na jihar Kano Hashimu Suleiman Dungurawa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano.
A cewar Dungurawa, an datakar da ‘yan majalisar dokokin ne a karkashin jam’iyyar NNPP amma a kwanakin baya sun tsunduma cikin ayyukan da suka saba wa muradu da akida da kuma ka’idojin jam’iyyar.
KU KARANTA: IPAC Tayi Allah Wadai Da Kalaman Batanci Da Yan Siyasa Ke Yiwa Juna A Kano
Ya ce an ba su tikitin takara a lokacin zabukan jam’iyyar, amma maimakon nuna godiya, sai suka yi ta ayyukan da suka ci karo da muradun jam’iyyar.
Rahotanni sun bayyana cewa dakatarwar tana da alaka da taron daurin auren Yar Sanata Kawu Sumaila da kuma kaddamar da ayyuka a jami’ar sa da ke Sumaila.
Dungurawa ya bayyana mamakinsa da cewa wadanda suka halarci taron galibinsu mutane ne da suka yi wa Kawu aiki a baya, yayin da ba a gayyaci ‘yan jam’iyya ba.
Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa za a kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da magance matsalar.
Duk da dakatarwar, Dungurawa ya jaddada cewa har yanzu akwai sauran damar tattaunawa, kuma idan ‘yan majalisar da aka dakatar sun tuba suka nemi gafara, jam’iyyar na iya tunanin dawo da su.