Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bawa al’ummar musulmi umarnin fara duban Jinjirin watan Ramadan daga gobe juma’a 29 ga Watan Sha’aban, 1446AH wacce ta yi dai-dai da 28 ga Fabarairun 2025.
Farfesa Sambo Wali Janaidu wanda shine shugaban kwamitin ganin wata na majalisar Mai alfarma sarkin Musulmi ne ya bayyana hakan cikin wata takarda wacce ya sanyawa hanu, aka kuma aikewa Yan Jaridu a Sokoto.
KU KARANTA: Muna Rage Farashi Man Girki a Watan Ramadan a Kasuwar Bello Road — Fatihu Iliyasu
Sanarwar ta bukaci al’ummar musulmi su fara duban Jinjirin watan a gobe juma’a sannan su kai rahoton ganin watan ga mai unguwa ko Dagaci ko hakimi ko kuma sarki mafi kusa da su.
Sanarwar ta yi fatan al’ummar musulmi za su gudanar da Azumin watan Ramadan cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.