• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Norway Ta Dakatar Da Siyarwa Jiragen Ruwan Amurka Mai Bayan Korar Zelensky Daga White-House

BySani Magaji Garko

Mar 1, 2025

Kamfanin siyar da mai na Jiragen ruwa na kasar Norway ya dakatar da siyarwa giragen ruwan Amurka mai biyo bayan korar shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky daga White-House.

Idan za’a iya tunawa a jiyar ne shugaban Amurka Donald Trump ya umarci shugaban Ukraine Zelensky da ya fita daga fadarsa biyo bayan tattaunawa mai zafi da Trump da Zelensky sukayi da nufin kawo karshen yakin Ukraine.

Jim kadan korar ne, kasashe da shugabanni a nahiyar Turai suka rika bayyana goyon bayan su ga Zelensky, suna mai cewa “Nahiyar Turai tana tare da mutanen Ukraine, da ma shugabansu.”

KU KARANTA: Yakin Rasha Da Ukraine: A Shirye Nake Na Tattauna Da Putin — Zelensky

Haltbakk Bunkers, kamfanin mai ya ce daga yanzu ya dena siyarwa da Jiragen ruwan Amurka mai.

Kamfanin ya kuma yi kira ga kamfanonin nahiyar Turai da su dena siyarwa Amurka man.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *