DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO
Mai martaba Sarkin Rano a jihar Kano Dakta Muhammad Umar ya bukaci mahukuntan hukumar Zakka da Hubusi ta Jihar Kano da su Fadada ayyukan su zuwa kananan hukumomi Jihar Kano 44 don tallafawa marayu da masu karamin karfin a fadin jihar.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana hakan a yayin da ya karbi bakuncin ayarin shugabannin Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano a Fadar sa dake Garin Rano.
Mai martaba ya ce inganta ayyukan hukumar zakka da Hubusi wata hanya ce da gwamnati zata bi domin tallafawa al’umma ta hanyar rage musu talauci da fatara.
Ya kuma bayyana cewa zakka wani Rukuni ne daga Rukunan addinin Musulunci don haka dole ne a bata kulawar data dace.
Dakta Umar ya sha al’washin yin duk mai yiwuwa don baiwa hukumar zakkar dukkanin wasu shawarwari da hadin kai da kuma goyon baya domin inganta aiyukansu.
Da yake Jawabinsa tunda farko, shugaban Hukumar Barista Habibu Dan Almajiri ya ce sun kai ziyara fadar Sarkin ne don neman cikakken goyan bayan Masarautar ta Rano domin inganta ayyukan hukumar kasancewar sarakuna sune iyayen kasa kuma sune sukafi kusanci da alumma.
Barista Dan Almajiri ya kuma yabawa Masarautar Rano bisa irin Tarbar da akayi Musu.