• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Rikicin Masarautar Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Dakatar Da Dawo Da Sanusi, Tana Jiran Hukuncin Kotun Koli

BySani Magaji Garko

Mar 14, 2025

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke ranar 10 ga watan Janairu wanda ya tabbatar da matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na gyaran dokar majalisar masarautun Kano ta shekarar 2019, har sai an yanke hukuncin daukaka kara a kotun koli.

Idan za’a iya tunawa, kotun daukaka kara da ke zamanta a Kano ta yi watsi da umarnin da Mai Shari’a Abubakar Liman na babbar kotun tarayya da ke Kano ya bayar a ranar 20 ga watan Yuni, inda ta soke matakai/hanyoyin da gwamnatin jihar Kano ta dauka bisa dokar masarautar Kano ta shekarar 2024, ciki har da nadin Muhammadu Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 16.

Kotun daukaka kara ta Kano da ta zauna a Abuja, ta ce hukuncin da ya soke matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka a karkashin dokar majalisar masarautu ta 2024 wacce mai shari’a Liman ya bayar da ita, kotun Bata da hurumin sauraroron karar.

KU KARANTA: KANO: Gidauniyar Zainab Suleiman Ta Fara Gina Cibiyar Koyar Da Sana’o’i Kyauta Ga Marassa Karfi a Danbatta

Da bata gamsu da hukuncin ba, gwamnatin jihar Kano ta daukaka kara zuwa kotun koli inda daga bisani ta shigar da kara a kotun daukaka kara inda ta bukaci kotun da ta dakatar da aiwatar da hukuncin har sai an yanke hukuncin daukaka kara a kotun koli.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma’a da wasu alkalai uku karkashin jagorancin Mai shari’a Okon Abang a kararraki biyu masu lamba CA/KN/27M/2025 da CA/KN/28M/2025, wanda Alhaji Aminu Babba Dan’agundi ya shigar a gabanta.

An shigar da karar ne a kan gwamnatin jihar Kano, da kakakin majalisar dokokin Kano, da babban sufeton ‘yan sanda na kasa, da hukumar tsaro da kare dukiyoyin al’umma wato “civil Defense”, da jami’an tsaron farin kaya, da sauran hukumomin tsaro.

Aminu Babba Dan’agundi (Sarkin Dawaki Babba), ya shigar da karar a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, inda ya bukaci a ba su umarnin hana wadanda ake kara aiwatar da hukuncin kotun daukaka kara a yayin da ake ci gaba da daukaka kara a kotun koli.

Dalilin da ya sa aka shigar da karar shi ne tun da farko wanda ya shigar da karar ya shigar da karar ne a Kano don kare masa hakkinsa, kotun da ke shari’ar ba ta da hurumin saurare da tantance karar, don haka akwai bukatar a hana wadanda ake kara aiwatar da hukuncin.

Bugu da kari, mai neman ya kara da cewa, dokar da majalisar dokokin jihar ta kafa ta 2024, wadda majalisar dokokin jihar ta amince da ita, kuma gwamnan ya Sanya mata hanu ta zama doka, ita ce ta bada dama aka rusa sabbin masarautun da aka kafa tare da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16.

A cikin hukuncin da suka yanke, Alkalan uku karkashin jagorancin Okon Abang, sun bayyana cewa wanda ya shigar da karar Yana da damar a kare masa mutuncinsa da saboda ya rike mukamai daban-daban.

Kotun ta ci gaba da cewa, bada umarnin ya zama dole “an ba da umarnin ne wacce zata kiyaye matsayinsa da kuma wakilin kotun da ta bada umarnin.

Mai shari’a Abang, da yake ba da umarnin, ya jaddada cewa tsarin mai neman ya dace kuma ya cika dukkan sharuddan doka da ake bukata don samun agajin da ake nema.

Ya yi nuni da cewa, an riga an shigar da kara mai inganci a gaban kotun koli, wanda ke karfafa bukatar kiyaye abin da ya shafi shari’ar. Bugu da ƙari, Kotun Daukaka Kara ta amince da haƙƙin kariyar da mai nema ke da shi, la’akari da cewa ya yi sarauta ta shekaru biyar kafin a cire shi.

Kotun ta hana wadanda ake kara aiwatar da hukuncin da aka yanke ranar 10 ga watan Janairu wanda ya soke rusa masarautun da gwamnatin jihar Kano ta yi. Har ila yau, ta ba da umarni, tare da ci gaba da kasancewa yadda ake har sai Kotun Koli ta yanke hukunci na karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *