Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya ce kasarsa ta yanke duk wata huldar Diflomasiyya da kasuwanci da kasar Belgium ba tare da Bata lokaci ba.
Paul Kagame ya zargi Belgium da sanyawa Rwanda takunkumai domin Karya tattalin arzikin Kigali.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake cigaba da samun tankiya tsakanin bangarorin biyu, biyo bayan zargin da ake yiwa Rwanda da daukar nauyin Yan tawayen M-23 da suke cigaba da addabar kasar jamhuriyar dumokuradiyyar Congo (DRC) wacce ta kasance kawa ga Belgium.
KU KARANTA: Nigeria da Kasashen Duniya 19 da Tsuke Bakin Aljihun Amurka Zaifi Shafa
A yayin da Rwanda ta sanar da korar jam’ian diflomasiyya na Belgium, ta kuma ce ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai sun sanya takunkumai kan mutum 9, cikin har da kwamandojin sojin Rwanda.
To Amma, gwamnatin kasar Belgium ta ce matakin na Rwanda bai dace ba, kuma ta ce za ta mayar da martani.
Ana dai zargin kasashen Rwanda da Uganda da kuma Burundi da goyon bayan M-23 din, zargin da suka sha musamtawa.
Wata kwarya-kwaryar bincike da GLOBAL TRACKER ta gudanar ya nuna cewa akwai sojojin Rwanda kusan 3,000 zuwa 4,000 da suke tallafawa M-23 Kai tsaye ko kuma ta wata hanyar daban.