Wata gagarumar Gobara da ta tashi a kasuwar Yan Gwan-gwan dake yankin unguwar zangon-Dakata cikin yankin karamar hukumar Nassarawa a Kano ta yi sanadin Kone kusan dukkan Kasuwar.
Gobarar wacce ta tashi a kusa da Ofishin hukumar WAEC na Kano ta yi saurin yaduwa a yankin lamarin da ya saka al’umma neman tallafi don kashe ta.
Wani bidiyo da GLOBAL TRACKER ta gani ya nuna yadda wutar ta da hayakin ta ke tsiri ta yadda ko Ina kake a karamar hukumar Nassarawa zaka iya hango ta.
KU KARANTA: Kungiyar Likitici Musulmi Ta Duba Daurarru 1,000 Da Basu Magani Kyauta.
GLOBAL TRACKER ta tuntubi mai magana da yawun hukumar kashe Gobara ta Jihar Kano Saminu Abdullahi inda ya ce hukumar ta tura jami’anta domin gano musabbabin afkuwar gobarar.
“Yanzu da muke magana da kai wannan hukuma ta tura jami’anta, saboda haka bazan iya gaya maka musabbabin afkuwar gobarar ba, amma idan sun dawo zasu bayyana dalilin afkuwar lamarin,” inji Saminu.