• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Barau Ba Ya Mutunta Jam’iyar APC Shi Yasa Ya Karbi Korarrun Jam’iyarmu a Gidan Sa — Shugaban SDPn Kano

BySani Magaji Garko

Mar 20, 2025

Shugaban jam’iyar SDP na kasa reshen jihar Kano ya ce matemakin shugaban majalisar Dattawa ta kasa Barau I. Jibrin baya Mutunta Jam’iyarsa ta APC shi yasa yake karya ka’idojin ta ciki harda karbar Korarrun Yan jam’iyar SDP a gidansa maimakon Ofishin jam’iyarsa.

“Ko da yake ba abun mamaki bane saboda sau da yawa mun sha jin Yan siyasa suna azo aje a wanki Gara, sai suje wajen Barau su ce masa sun fita daga wata jam’iyar sun koma APC shi kuma sai ya dauki kudaden ya basu, sannan su dawo Kano ko gidajen su tare da cigaba da sabgogin da suke yi a jam’iyun su na asalin,” Inji Ali Shattima Tudun Murtala, Shugaban jam’iyar SDP na Jihar Kano.

Ali Shatima ya bayyana hakan a taron manema labarai a Kano, wanda yake a matsayin martani da ikirarin wasu yan takara biyu da suka yi na barin jam’iyar SDP.

KU KARANTA: Mun Karbi Yan APC Sama Da 200,000 a NNPP Daga Kananan Hukumomi 11 a Kano — Kwankwaso

Idan za’a iya tunawa, a yan kwanakin nan ne tsohon dan takarar gwamnan Kano a SDPn Bala Muhammad Gwagwarwa da Yusuf Salisu Buhari, dan takarar matemakin shugaban Kasa na jam’iyar a zaben 2022 suka bayyana fitarsu daga jam’iyar SDP zuwa APC mai mulkin Nigeriya, suna zargin cewa ba’a yi musu adalci ba, kuma shigar tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i cikinta zai janyo matsala a cigaban ta.

To amma, shugaban na SDP a Kano ya ce dama can Bala Gwagwarwa da Salisu Buhari Korarru ne a jam’iyar ta SDP.

“Shi Bala Gwagwarwa dama korarren jam’iyar SDP ne tun kafin zabe saboda baima sayi form na takara ba, kuma bai tabuka komai a jam’iyar ba, bashi da office na yakin Neman zabe a mazaba ko matakin jiha idan kuma akwai wanda zai iya nunamin zan bashi naira miliyan Daya (1,000,000.00), saboda haka tun kafin ayi zabe muka Koro Bala Gwagwarwa daga SDP kuma har yanzu korarre ne tunda bai rubuto takardar namen afuwa ba. Shima Salisu Buhari korarre ne saboda Muna zarginsa da yayi wa jam’iyar SDP Zagon Kasa (Anty-party) saboda ya zabi wata Yar takarar Sanata a wata jam’iyar da ba SDP ba, saboda haka su yi ikirarin sun fita daga SDP zancen banza ne, saboda dama ba Yan jam’iyar bane,” inji Shattima.

“A iya tunanina jam’iyar APC ce zata karbe su tun daga mataki na mazaba har zuwa jiha, amma sai gasu a gidan Sanata Barau Jibrin, kaga kenan Shima Barau baya Mutunta Jam’iyarsa ta APC domin shugabancin jam’iya ne ya kamata ya karbe su ba wani mutum ba ko Dan takara,” inji Shattima.

Ali Shattima ya kuma bayyana cewa shigar tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufa’i cikin SDP babban cigaba ne saboda El-Rufa’i hazikin Dan siyasa mai rajin cigaban Arewacin Nigeriya baki daya.

KU KARANTA: Dungurawa Bashi Da Hurumin Dakatar Da Ni ko Kabiru, Sanata Doguwa Ne Halastaccen Shugaban NNPP a Kano — Kawu Sumaila

“El-Rufa’i Alheri ne, El-Rufa’i Mai son cigaban Talakawan Nigeriya ne, kai ba don jajircewa irin ta su El-Rufa’i na Kaduna ba da irin cin kashin da gwamnatin Bola Tinubu za ta yiwa wannan yankin sai kasha mamaki,” inji Shattima.

Shugaban ya kuma ce har yanzu shugabanni jam’iyar SDP na Jihar Kano suna nan a matsayin su kuma suna aikin su yadda yakamata ya na mai cewa Bala Gwagwarwa da Salisu Buhari wasu Mutane ne da basu da katabus kuma su ka dai suka koma APCn Barau Jibrin ta bogi.

Ya kuma ce dukkan Yan takara na jam’iyar daga matakin kansiloli, zuwa majalisar tarayya suna nan a jam’iyar ta SDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *