• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Gwamnan Kano Da Jigawa Sun Halarci Jana’izar Mahaifiyar Dikko Radda

BySani Magaji Garko

Mar 23, 2025

Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da Umar Namadi na Jigawa na cikin mayan mutanen da suka Halarci Jana’izar Hajiya Safara’u Umaru Baribari, mahaifiyar gwamnan Jihar Katsina Dikko Umar Radda.

Jana’izar wacce akayi a Kauyen Radda dake yankin karamar hukumar Charanchi ta Jihar Katsina ta samu halartar sanannun mutane ciki harda sarakunan gargajiya.

Cikin jami’an gwamnatin Katsina da suka Halarci Jana’izar akwai matemakin gwamnan Katsina Malam Faruq Lawal Jobe da shugaban majalisar dokoki Jihar Nasiru Yahaya Daura da ‘yan majalisu da sakataren gwamnatin Jihar Barista Abdullahi Garba Faskari da shugaban ma’aikata da sauran jami’an gwamnati.

KU KARANTA: Wata Mata ta Yanke Gaban Mijin ta a Daren Farko a Katsina

Sauran jami’an sun hada da tsohon matemakin gwamna Tukur Ahmed Jikamshi da Sarkin Katsina Abdulmumin Kabir Usman da takwaransa na Daura Alhaji Faruq Umar Faruq da shugaban jam’iyar APC Alhaji Sani Aliyu da sauran jama’a da dama.

Babban limamin Katsina Imam Gambo Mustapha ne ya jagoranci Jana’izar wacce ta samu halartar dumbin mutane ciki harda Alhaji Kabir Umar Dagacin garin Radda kuma Da ga marigayiya wanda yake karbar gaisuwa a madadin dukkan Iyalan marigayiyar.

An dai gudanar da addu’o’i na musamman ga marigayiya da sauran musulmi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *