Gwamnatin Tarayya ta bada umarnin a Binciki musamman da ya janyo fasa gidan Ajiya da gyaran Hali na Koton Karfe dake Jihar Neja.
Ministan cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ya yi Allah-wadai da fasa gidan inda ya ce gwamnatin za ta yi amfani da bayanan da take da su da kayan aiki wajen dawo da mazauna gidan da suka tsere.
Babatunde Alao, wanda shine mai magana da yawun ministan cikin wata sanarwa da ya bayar a yau Litinin, ya ce ministan ya umarci mai rikon mukamin shugaban hukumar Ajiya da gyaran Hali na kasa Sylvester Ndidi da ya ziyarci gidan don tattara bayanai da kuma gano dalilin da suka janyo afkuwar lamarin.
KU KARANTA: LABARI-DA-HOTUNA: Yadda Aka Nada Ibrahim Yaro D/tofa Talban Alajawa a Bagwai
Idan za’a iya tunawa dai, aƙalla fursunoni 12 ne suka tsere baya sun fasa gidan yarin gwanmatin Najeriya da ke garin Koton-karfe a jihar Kogi.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ƙara da cewa tuni sun sake kama fursuna ɗaya daga cikin waɗanda suke tsere ɗin.
Gwamnatin Kogi ta ce za ta haɗa ƙarfi da ƙarfe da jami’an tsaro domin gano yadda fursunonin suka samu nasarar tserewa a safiyar yau ranar Litinin.
Kwamishinan ya bayyana lamarin da abin takaici, “sannan yadda fursunonin suka iya tserewa ba tare da barin wata alama ba abin tambaya ne.
Ya ce dole a gudanar da bincike mai zurfi, sannan a kamo fursunonin da suka tsere, sannan a gano waɗanda suke da hannu,” in ji Fanwo.