A kokarinsu na cigaba da bunkasa harkokin addinin musulunci a fadin Nigeriya, hukumar Shari’ah ta jihar Kano haɗin guiwa da kungiyar Musulmi matasa da Duniya wato “World Assembly of Muslim Youth (WAMY) sun shiryawa wadanda suka karbi addinin Musulunci shan ruwa a harabar hukumar dake Kano
An gudanar da Shan ruwan ne a ranar Lahadi 23 ga Ramadan a harabar hukumar karkashin Jagorancin Mukaddashin Shugabanta Sheikh Ali Dan-abba.
A yayin taron ne, hukumar ta ayyana cewa daga yanzu zata rika gudanar da taron Shan ruwan a ranar 15 ga Ramadan na kowacce shekara da wadanda suka karbi addinin musulunci a cikin shekarar.
KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya Ta Umarci A Binciki Fasa Gidan Yarin Koton Karfe
Sheikh Ali Dan-abba ya kuma mika godiya ga gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf da Kungiyar WAMY da suka basu gudummawa wajen shirya wannan taro.
Cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan yada labarai da wayar da kan jama’a na hukumar Musa A. Ibrahim (Best Seller) ya aikowa GLOBAL TRACKER ta ce taron Shan ruwan ya sami halartar dukkanin shugabannin hukumar da mambobinta da kuma ma’aikatanta tare da shugabannin kungiyar Wamy da wasu manyan mutane da suka zo.
Shima wakilin shugaban kungiyar Wamy Alhaji Sanusi ya nuna jin dadinsa da yadda wannan shan ruwa ya faru, kuma ya tabbatar da cewar kungiyar su ƙungiya ce ta taimakon addinin musulunci da musulmi a ko ina suke, kuma kungiyar zata ci gaba da wannan aikin alherin da izinin Allah.
Daga daga cikin yaran da suka rabauta da addinin musulunci akwai Aisha Suraj ta ce sun ji dadin yadda ake karramasu da suna kuma jindadi da yadda mutane suke jansu a jiki babu nuna banbanci ko kyama “Lalle addinin Musulunci addini ne mai dadi”
Shugaban hukumar Dr. Sani Ashir ya godewa Allah da kuma kira ga masu hannu da shuni da su kawowa wadannan yara tallafi domin kara karfafarsu akan addini, sannan kuma ya bada tabbacin cewar shirin an yi shine a kure amma shekara mai zuwa da yardar Allah za a ga shiri na musamman.
A karshe kwamishina na daya a hukumar Gwani Hadi yayi kira da al’umma da su zo domin auren wadannan yara domin babu irin kalar da ba’a da ita a hukumar, inda yayi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano da kasa baki daya.