• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Kungiyar Salanta A Yau ta Raba Kayan Sallah Ga Marayu Sama Da 200

BySani Magaji Garko

Mar 25, 2025

DAGA: ASHIRU GIDAN TUDU, KANO

A wani yunkuri na taimako da jin-kai ga marayu da masu karamin karfi, kungiyar Salanta A Yau dake yankin karamar hukumar Birnin Kano da kewaye, ta rabawa yara maza da mata sama da 200 tallafin kayan Sallah domin gudanar da bukukuwan sallarsu kamar yadda masu iyaye ke yi.

An gudanar da rabon kayan sallah ne a tsakiyar unguwar Salanta kan Labi a safiyar Talatar nan.

Tun da fari da yake jawabi a wajen taron, shugaban kungiyar ta Salanta a Yau Malam Ahmad Muhammad Mika’il ya bayyana cewa an shirya taron ne domin taimakawa yara marayu da marasa karfi.

KU KARANTA: Cibiyar Kamaludden Nama’aji Dinkawa Marayu 100 Kayan Sallah

Da yake jawabi, mai unguwar Duka-wuya Salanta Malam Magaji Garba ya nuna jin dadinsa da tallafin da kungiyar ta bayar tare da yin kira ga dukkanin alummar unguwar musamman masu hannu da shuni dasu cigaba da tallafawa yunkurin kungiyar da dukkanin abun data ke bukata domin gudanar da harkokinta na yau da kullin.

Daga bisani iyayen marayun da suka rabauta da kayan wadanda Hadiza Isyaku Abdullahi ta tayi jawabi a madadinsu sun yi godiya ga kungiyar ta Salanta A Yau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *