• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Sarkin Kano Na 15, Aminu Ado Ya Soke Dukkan Bukukuwan Sallah, Ya Ba Da Dalilai

BySani Magaji Garko

Mar 27, 2025

Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke duk wasu shirye-shiryen gudanar da Bukukuwan Sallah karama a fadin jihar Kano.

Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a cikin wani dan takaitaccen faifan bidiyo a daren Larabar nan, inda ya bayyana dalilan da suka sa aka dakatar da shirin hawan.

Idan dai za a iya tunawa, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da jami’an tsaro musamman rundunar yan sanda ta kasa shirinsa na gudanar da bukukuwan Sallah.

KU KARANTA: Sarkin Bade na Kaduna ya Ziyarci Sarkin Kano Don Yin Mubaya’a

Idan kuma za’a iya tunawa, Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umarci mai martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II tare da sarakuna masu Daraja ta biyu da su shirya don gudanar da Bukukuwan Sallah karama a fadin jihar Kano baki daya domin tunawa.

Hakan dai ya haifar da tashin hankali da zaman Dar-dar da kuma tunanin abinda kaje ya zo lamarin da ya sa ‘yan sanda suka baiwa jama’a tabbacin kare rayuka da dukiyoyin su kafin da kuma bayan bukukuwan karamar Sallah.

Aminu Ado ya bayyana a cikin faifan bidiyon cewa ya soke bikin ne saboda kokarin da wasu malaman addinin musulunci masu daraja da kuma dattawa suka yi wajen ganin an samu zaman lafiya.

“Dole ne mu dakatar da shirin gudanar da wannan al’amari sakamakon shawarwari da malaman addinin Musulunci masu daraja da kuma dattawa suka bamu,” inji Aminu Bayero.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *