• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Ku Fara Duban Watan Sallah — Sarkin Musulmi

BySani Magaji Garko

Mar 28, 2025

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya umarci al’ummar musulmi a fadin Nigeriya da su fara duban watan Shawwal (Watan karamar Sallah) a gobe Asabar 29 ga watan Ramadan, 1446 wacce ta yi dai-dai da 29 Maris, 2025.

Farfesa Sambo Wali Janaidu, shugaban kwamitin ganin wata na fadar Sarkin Musulmi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikewa Yan Jaridu a Sokoto ranar Juma’a.

Farfesa wanda shine Waziri Sokoto ya kuma bukaci al’umma da su kai rahoton ganin watan ga fadar sarakunan gargajiya mafi kusa da su domin sanar da Sarkin Musulmi.

KU KARANTA: Mun Katse Duk Wata Huldar Diflomasiyya Da Kasar Belgium — Shugaban Rwanda

Sanarwar ta kuma da al’umma da su kira lambobin waya: 08037157100 ko 08066303077 ko 08035965322 ko 08099945903 ko kuma 07067146900 domin sanar da fadar Sarkin Musulmi Kai tsaye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *