Rundunar ƴan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta haramta gudanar da bukukuwan Sallah a fadin jihar.
Kwamishinan ƴan sandan Jihar Kano Ibrahim Adamu Bakori ne ya sanar da haka yayin taron manema labarai da ya gudana a hedkwatar ƴansandan jihar da ke Bompai yau Juma’a.
Bakori lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai ya jaddada muhimmancin zaman lafiya a yayin bukukuwan Sallah ƙarama a bana.
KU KARANTA: Sarkin Kano Na 15, Aminu Ado Ya Soke Dukkan Bukukuwan Sallah, Ya Ba Da Dalilai
A cewarsa, bayanan tsaro sun nuna ƙarin fargaba da ake fuskanta da kuma barazana da hawan Sallah zai fuskanta abin da ka iya haifar da matsala.
“Bayan tattara bayanan tsaro rahotanni sun nuna akwai shiri mara kyau da ake na kawo tazgaro ga hawan Sallah, don haka rundunar ta tuntubi gwamnatin Kano da sauran masu ruwa da tsaki kuma mun yanke hukuncin dakatar da dukkanin hawan sallah a jihar”
Kwamishinan ƴan sandan na Kano ya kuma buƙaci al’umma a jihar da su bai wa jami’an tsaro haɗin kai don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.