Rundunar yan sandan ta kasa ta gayyaci sarkin Kano Muhammadu Sanusi II bisa zargin karya dokar da ta saka na hana gudanar da hawan a lokutan bukukuwan karamar Sallah.
A cikin wasikar gayyatar mai lamba CR:3000/FID/FHQ/ABJ/VOL59/697 mai dauke da kwanan watan 2, Afirilun 2025, kwamishinan ƴan sanda Olajide Rufus Ibitoye ne ya sanya mata hanu a madadin matakin babban sifeton yan sanda mai kula da tattara bayanan sirri a rundunar yan sanda ta kasa dake Abuja ne.
“An umarceni na sanar da kai cewa babban sifeton yan sanda na kasa ta hanun mataimakinsa suna gayyatar ka a cigaba da gudanar da binciken da ake yi game da abinda ya faru a lokacin bukukuwan sallah a yankin ka,” inji takardar.
Ana sa ran sarkin na Kano zai halarci shalkwatar rundunar yan Sanda ta kasa dake Abuja da Karfe 10:00am a ranar Talata 8, Afirilun 2025.
KU KARANTA: Galadiman Kano Abbas Sanusi Ya Rasu
Sanarwar ta ce ana sa ran sarkin zai bada wasu bayanai ne wanda zasu taimaka a cigaba da binciken da rundunar ta ke yi.
Gayyatar sarkin na zuwa ne bayan rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta kafa kwamitin mutane 8 domin gudanar da binciken kisan wani jami’in Vijilanti a ayarin sarkin a lokacin hawan Sallar.