Wani ruwan sama mai karfi kamar da bakin kwarya yayi sanadin rushewar gidajen da ba’asan adadinsu ba a karamar hukumar Uromi Esan ta Arewa a jihar Edo.
Rushewar gidajen na zuwa ne kusan mako biyu bayan da wasu Yan Vijilanti suka tare Yan Arewacin Nigeriya tare da yiwa 16 daga cikinsu kisan wulankaci gami da Kone gawarwakinsu.
Wani Mazaunin garin Malam Yusuf ya tabbatarwa da jaridar GLOBAL TRACKER faruwar lamarin cikin Daren lahadin nan abin ya faru.
KU KARANTA: Rundunar Sojin Nigeriya ta Haramta Amfani Da Jiragen Daukar Hoto a Arewa Maso Gabas
Ya ce har ya zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wanda ya san adadin gidajen da muka rushe.
Bayanai da wannan jarida ta samu sun tabbatar da faruwar lamarin.
Shima wani Malam Salisu Mazaunin garin ya tabbatarwa da GLOBAL TRACKER cewa mutane biyu sun mutu sanadi’yyar ruwan saman.
Hakazalika, kwamared Kabiru Sani, sakatare janar na gamayyar kungiyoyin Arewacin Nigeriya dake Jihar ta Edo a yanzu haka wanda ke bibiyar abubuwa da suka faru ya yankin na Uromi ya tabbatarwa da GLOBAL TRACKER lamarin.
Akwai Karin bayani…….