DAGA: ABDULLAHI ALHASSAN, KADUNA
Gwamnan Jihar Kaduna Alhaji Uba Sani ya kaddamar da shirin sarrafa amfanin gona na musamman Irinsa na farko a Najeriya—Special Agro-Industrial Processing Zone (SAPZ).
Ana sa ran shiri mai tarihi da zai sauya tsarin noma, fitar da dubban mutane daga talauci ya kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.
An kaddamar da shirin ne da wani kaso daga cikin dala miliyan 520 da Bankin Raya Afirka (AfDB), Bankin Raya Musulunci, Asusun Raya Aikin Noma na Majalisar Dinkin Duniya (IFAD), da Gwamnatin Tarayya suka ware domin kafa irin wannan tsari a jihohin Najeriya da dama.
KU KARANTA: Manoma Na Fargabar Cigaba Da Asara Sakamakon Karancin Ruwa a Kano
Kaduna na cikin jihohin farko da suka fara cin gajiyar shirin.
A wajen kaddamarwar, Shugaban bankin raya kasashen Afirka AfDB, Dokta Akinwumi Adesina, ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa fifita harkar noma da samar da shugabanci irin na gina al’umma, inda ya bayyana gwamnatin Kaduna a matsayin “gwamnati mai sauraro da kuma aiwatarwa.”
Shi dai shirin SAPZ zai mai da hankali kan sarrafa amfanin gona irin su masara, shinkafa, waken soya, rogo, kaji, da dabbobi.
A karkashin shirin ana sa ran za’a samar da fiye da ayyuka 500,000 a Kaduna kadai, tare da amfani ga fiye da manoma 100,000 ta hanyar bunkasa hanyoyin kasuwa, fasaha da kayayyakin more rayuwa.
Gwamna Uba Sani ya bayyana shirin a matsayin “mai sauya tarihi”, yana cewa: “Wannan shiri zai bude mana kofar bunkasar noma, rage talauci a karkara, da samar da hanyoyin rayuwa masu dorewa.”
Tsarin SAPZ yana mai da hankali ne kan tattara masana’antun sarrafa amfanin gona a wuraren da noma ke da karfi, don rage ire-iren asarar dake biyo bayan girbi; kara yawan amfanin gona, da jawo jari daga masu zaman kansu.
Wannan SAPZ da aka kaddamar a Kaduna na zaman wata babbar dama a kokarin Najeriya na cimma wadatar abinci, sauya rayuwar manoma, da bunkasa tattalin arzikin al’ummar karkara.