• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Muna Allah-wadaran, Tir Da Hukuncin Kotun ECOWAS — Samarin Tijjaniyyar Nigeriya

BySani Magaji Garko

Apr 15, 2025

A wani mataki na maida martani da kuma bayyana matsayin ta, kungiyar samarin Tijjaniyya ta Nigeriya ta yi Tir da Allah-wadai da hukuncin da kotun kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta yi game da mutanen da sukayi Batancin ga Annabi Muhammad S.A.W.

Idan za’a iya tunawa kotun kungiyar ECOWAS ta bukaci gwamnatin tarayyar Nigeriya da ta dena yanke hukuncin kisa ga mutanen da aka samun da laifin Batancin ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW.

Amma, a martanin da ta mayar, kungiyar ta samarin Tijjaniyya ta ce hukuncin ya sabawa dokokin addinin musulunci wanda mafi yawan na mutanen Nigeriya suka yadda da shi a matsayin addinin su, kuma addinin su ya wuce/Yana gaba da komai da kowacce doka.

KU KARANTA: DA DUMI-DUMI: Yunkurin Juyin Mulkin Nijar; An Fara zanga-zangar Goyon Bayan Bazoum, An tarwatsa masu zanga-zangar

A wata sanarwa da Kungiyar ta fitar Mai dauke dasa hannun Babban Sakatare Shehu Tasiu Ishaq da sakataren yada labarai Abubakar Balarabe Kofar Naisa Kungiyar tayi tir da Allah wadai da Hukuncin.

Kungiyar ta ce duk wani hukuncin da zaici Karo da dokokin Ubangiji bazasu goyi bayansa ba.

Daga nan kungiyar samarin Tijjaniyya ta kasa tayi kira ga Gwamnati a kowane mataki da lallai a tabbatar dabin dokokin da suka tabbatar da tsarin addinin musulunci akan duk wanda ya keta alfarmar fiyayyen halitta kamar yadda yake a kundin dokokin shari’ar Musulunci.

Kungiyar kuma ta yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa yadda ta jaddada matsayinta na tabbatar da dokokin da suka shafi hukunta duk Wanda yayi batanci ga Janibin Annabi muhammadu SAW Wanda daman tuni dokokin sun kasance na Gwamnatin Jihar ne.

A don hakane ma Kungiyar ta sake jaddada bukatar mabiya dariqar Tijjaniyya da sauran al’umar Musulmi su cigaba da kasancewa masu son zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bin dokokin addinin musulunci.

Kungiyar ta sake bukatar Musulmi su dunga kasancewa masu yin ladabi da biyayya tare da kare duk wata martaba ta Janibin Annabi muhammadu SAW a kalamansu na yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *