• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Shugaban APC, Ganduje Ya Yi Ganawar Sirri Da Kawu Sumaila, Ali Madaki Da Sauran Yan NNPP

BySani Magaji Garko

Apr 15, 2025

Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma shugaban jam’iyyar APC Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wata ganawar sirri da wasu manya cikin jam’iyyar NNPP mai mulkin Jihar Kano.

Cikin wadanda aka yi ganin akwai Sanata Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila da Hon. Ali Madaki sai Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da kuma Hon. Badamasi Ayuba.

Mai taimakawa Ganduje kan harkokin daukar hoto Aminu Dahiru ne ya tabbatar da ganawar.

Ana dai ganin ganawar a matsayin wani mataki na sake hadewar ya’yan jam’iyyar ta NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulkin kasa a yanzu.

Ya zuwa yanzu, GLOBAL TRACKER bata san abubuwan da aka tattauna ba.

Akwai Karin bayani…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *