• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

KANO: ‘Kwanakin Mu 33 Bamu Da Wutar Lantarki a Gwale’

BySani Magaji Garko

Apr 16, 2025

Mazauna unguwar Lokon Makera a yankin karamar hukumar Gwale dake cikin kwaryar Birnin Kano sun koka kan yadda suke shafe sama da kwanaki 33 basa samun wutar Lantarki duk da kasancewar su a cikin kwaryar Birnin Kano.

Daya daga cikin Malaman Addinin musulunci a yankin Malam Dauda lokon Makera ne ya bayyana hakan a wani rubutaccen sakon korafi da ya aikowa GLOBAL TRACKER.

Malamin ya ce abin takaici ne yadda mutanen yankin suke fama da matsalar wuta tun cikin Azumin watan Ramadan har zuwa yanzu duk da kasancewar su cikin kwaryar Birnin Kano.

KU KARANTA: Ministan Man Fetir Ya Yabawa NNPC Kan Aikin Samar Da Wutar Lantarki a Maiduguri.

Malamin ya yi zargin nuna halin ko-in-kula daga shugabanni yankin musamman Yan siyasa da suka hada da Yan majalisar tarayya da takwaransa na majalisar dokokin Jihar Kano ya na mai cewa “mafi yawan al’umma ba su ma san wadanda ke wakiltarsu a yankin ba kuma cikinsu harda ni duk da kasancewata malamin Addinin musulunci kuma dan boko”.

Dauda lokon Makera ya bukaci kamfanin rarraba hasken wutar Lantarki na jihohin Kano, Jigawa da Katsina KEDCO da ya kaiwa al’ummar yankin dauki.

Malamin ya ce matukar Yan siyasa a Gwale suka gaza warware matsalolin da mutane ka fama da su akwai ranar kin dillanci, ranar da kwanne dan siyasa zai je da bukata kuma al’ummar su yi watsi da bukatarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *