A wani mataki na kare lafiyar al’umma don samun cigaba, gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za ta dauki matakin kashe Ɓeraye a karamar hukumar Garun Malam domin dakile yaduwar Zazzabin Lassa.
Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa wanda shine mai magana da yawun ma’aikatar lafiya ta Jihar Kano ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikowa GLOBAL TRACKER.
Sanarwar ta ce kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana hakan inda ya ce daukar matakin ya zama wajibi kuma mataki na gaggawa domin kare lafiyar al’umma, ganin yadda aka tabbatar da bullar cutar Lassa a Garun Malam, wacce ta yi sanadin rasuwar wata baiwar Allah.
KU KARANTA: Mutane Sama Da 340 Sun Kamu Da Cutar Kwalara a Sudan
Kwamishinan ya bayyana cewa tuni aka killace duk masu mu’amala da mamaciyar, ciki har da mijinta da kuma jami’an lafiyar da suka kula da ita lokacin da aka kawo ta asibiti.
Binciken da aka gudanar ya tabbatar da cewa mijin marigayiyar da daya daga cikin yaranta sun kamu da cutar.
Dr. Labaran ya jaddada cewa kashe Ɓerayen da ke yankin da abin ya shafa wani muhimmin mataki ne na dakile yaduwar cutar, kasancewar Ɓeraye na daga cikin manyan hanyoyin yada cutar Lassa.
Gwamnatin ta kuma ja hankalin mafarauta da su guji farautar Ɓeraye, da kuma daukar matakan kariya domin hana yaduwar cutar daga jikinsu zuwa ga mutane.
Kwamishinan ya shawarci jama’a da su rika hanzarin sanar da jami’an lafiya mafi kusa idan suna da wani zargin cutar Lassa. Haka zalika, ya bukaci jami’an lafiya da su dauki matakan kariya yayin da suke kula da masu fama da cutar, domin kauce wa yada ta.