• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Gobara Ta Kone Bangaren Shagon Yar Tiktok Rahama Sa’idu Da Aka Rushe A Kano

BySani Magaji Garko

Apr 18, 2025

Gobara Ta Kone Bangaren Shagon Yar Tiktok din nan Rahama Sa’idu da aka rushe wanda a jiya Alhamis.

Idan ba’a manta ba dai jiya Alhamis ne hukumar rayawa da tsara birane ta Jihar Kano KNUPDA ta rushe gaban shagon wanda aka gina ba bisa ka’ida ba.

Shagon dai na kan titin UDB dake yankin karamar hukumar Tarauni a Kano.

KU KARANTA: ‘Za Mu Kashe Beraye A Kano Don Dakile Yaduwar Zazzabin Lassa’

Duk da yake baa tabbatar da musabbabin afkuwar gobarar ba, amma wasu rahotanni sun ce gobarar ya faru ne sakamakon aikin walda da ake yi a kusa da inda aka rushe ginin.

Wani shidar gani da Ido ya ce daya daga cikin shagunan da aka yi rusau din ne ya dauko hayar mai walda domin gyara inda akayi rusau din lamarin da ya janyo afkuwar gobarar.

Haka kuma rahotanni sun ce bayan shagon nata, wani shagon daukar hoto ma abin ya shafe su.

Yan sanda dai sun rufe gurin don gudun satar kayayyakin jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *