• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Zakka, Hubusi, Wakafi Da Yadda Zamu Inganta Rayuwar Al’ummar Kano — Barista Dan Almajiri

BySani Magaji Garko

Apr 23, 2025

DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO

Hukumar Zakka da Hubusi ta jihar Kano ta gabatar da taron wayar da kan al’umma akan ayyukan da suka shafi hukumar da suka hadarda Zakka, hubusi da wakafi da yadda ya kamata a gudanar su domin inganta Rayuwar alumma.

A lokacin taron wanda ya gudana ne rufaffen dakin taro dake harabar masallacin juma’a na sheikh Ahamadu Tijjani dake kofar mata acikin Birnin Kano, shugaban hukumar Zakka da hubusi Shaik Barrister Habibu Muhammad Dan almajiri Fagge ya bayyana cewa an shirya taron ne domin wayarwa da mutane kai akan muhimmanci bayar da zakka da taimakon juna da kuma tallafawa masu karamin karfi dake cikin al’umma.

Ya ce hukumar ta sha alwashin hada hannu da masana dake ciki da wajen Nigeriya domin kara wayar da kan alumma a game da abunda ya shafi zakka da hubusi da kuma wakafi ta yadda zai taimakawa gwamnati wajan rage Talauci da fatara da alumma suke fama dashi kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

KU KARANTA: Ku Fadada Ayyukan Bada Zakka Zuwa Kananan Hukumomin Kano 44 — Sarkin Rano

Shima a nasa jawabin, babban limamin masallacin juma’a na Alfurqan dake Nasarawa GRA Sheikh Dakta Bashir Aliyu Umar yayi cikakken bayyani akan Abunda ya shafi wakafi da kuma Hubusi da yadda ya samu asalin a addinin musulunci, da kuma irin gagarumar gudunmawa da suke bayarwa wajen bunkasa tattalin arzikin alumma da kuma ragewa gwamnati nauyi ta hanyar daukar nauyin marasa karfi da basu tallafi ta bangarori daban daban.

Dakta Bashir ya ce duk wani aikin da dan Adam ya gudanar lokacin da yake raye bayan ya mutu aikin zai tsaya amma idan ya samar da hubusi da wakafi zai cigaba da samun lada ko da bayan ya rasu kamar yadda addini ya tsara.

Da yake tsokaci, Dakta Nura Abdullah Babban malami a tsangayar koyan harkokin addinin musulunci dake jami’ar Bayero ya ce muddin gwamnati jihar kano ta baiwa hukumar zakka da hubusi goyan bayan da ya dace ita kanta zata samu sauki wajen sauke nauyin da yake kanta domin mutane da dama zasu samu saukin rayuwa a karkashin Hukumar.

Ya Kuma ja hankalin hukumar Zakka da hubusi ta jihar Kano da ta tashi tsaye wajen cigaba da wayar da kan al’umma akai akai a game da muhimmancin samar da wakafi da Hubusia cikin rayuwar alumma.

Taron ya samu halartar manyan malamai da dama Wadanda suka hadar da shugaban majalisar limaman juma’a na jihar Kano sheikh mahmad Adam da Dakta Mujitaba Abubakar Ramadan da malam Nura Arzai da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *