Gwamnatin jihar Kano ta nanata kudirinta naci gaba da bunkasa rayuwar jama’arta ta hanyar biyansu diyar aikin hanya na gwamnatin tarayya, Wanda ya taso tun daga Kabuga zuwa Rimin Gado zuwa Gwarzo zuwa Dayi a karamar hukumar Kankara dake Jihar Katsina.
Tun da farko da yake jawabinsa ga al’ummar wadan nan yankuna, Kwamishinan ayyuka na musamman Alhaji Nasiru Sule Garo, ya ce bijiro da biyan kudade da gwamna ya sahale a biya ya nuna karara irin jajircewarsa da kuma tausayawa al’umma a duk sanda wani abu ya gifta wanda ya ke bukatar daukin gaggawa.
Haka Kuma Kwamishinan ya kara da cewa an samar da wannan jimillar Kudin ne Sama da naira biliyan biyu ga al’umomin wadan nan kananan hukumomin da suka hada da Ungogo da Tofa da Rimin Gado da Kabo harma da karamar hukumar Gwarzo domin tallafa musu sakamakon aikin hanyar da yabi ta kan kadarorinsu.
Biyan diyyar ana sa ran zai kawo karshen tafiyar hawayniya da aikin yakeyi musamman don kaucewa hadurra da suke faruwa yanzu haka akan hanyar da kuma wahalhalun da masu amfani da hanyar da kuma mutanen garuruwan da suke kan hanyar suke ciki.
Kwamishinan ya ce tuni Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da fara biyan kudaden ba tare da Wani bata lokaci ba, ga jama’ar da aikin ya shafa kamar yadda aka tsara kuma jama’a tuni sun fara karbar hakkokin nasu.
Harwa yau Garo ya bukaci al’umomin da aka tantance domin cin gajiyar wannan diya da har yanzu basu amshi kudin suba dasu je da cikakkun hujjojinsu da sauran takaddun mallaka domin karbar kudadensu.