A karon farko tun bayan fara yaki tsakaninsu a shekarar 2022, shugabanni kasashen Rasha da makwabciyarta Ukraine sun zasu fara zama tsakaninsu kai tsaye domin kawo karshen yakin.
Za’a fara tattaunawar ne a kasar Turkiyya.
An taba gudanar da tattaunawar kawo ƙarshen yakin Rasha da Ukraine a manyan biranen ƙasashen. Wato Moscow da Kyiv, da kuma Washington da Riyadh na Saudiyya, baya ga wasu ƙasashe a nahiyar Turai.
KU KARANTA: Yanzu Babu Shirin Yiwa Ukraine Rejista A NATO — Mark Rutte
Yanzu dai hankula sun koma birnin Santambul na Turkiyya, ƙasar da ta ce tattaunawar za ta kasance cigaban wancan tattaunawar da aka fara yi a cikinta ne.
Ana sa ran sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio da jakadun ƙasar na musamman, Steve Witkoff da Keith Kellogg su halarci zaman, a wata alamar farko ta yunƙurin sUlhunta rikicin, bayan tsaiko na makwanni.
Shugaban Rasha Vladimir Putin, wanda ke fuskantar matsin lamba daga Amurka da Turai akan tsagaita wuta na kwanaki 30, ya gabatar da tayin tattaunawa ta kai tsaye tsakanin waƙilan Rasha da Ukraine a Turkiyya a wannan Alhamis.
Ya ɗauki wannan mataki ne duk da cewa masu fashin baƙi a Rasha sun shafe makwanni su na ta yaɗa hasashen cewa tattaunawar da Ukraine ba zata yiwu ba duba da yadda ake ƙoƙarin cewa shugaban Zelensky na Ukraine ba halastaccen shugaba ba ne.