Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da wasu manyan fina-finan Hausa a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood guda 22 daga sakasu a kafafen Internet ko gidajen Talabijin a kokarinta na tabbatar da ana bin dokar tace fina-finai sauda kafa tare da kara dora masana’antar a kan saiti.
Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ce ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya aikewa Yan Jaridu.
Sanarwar ta ce hukumar karkashin jagorancin Abba El-mustapha ta dauki gabarar tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai batare da cika ka’idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowanne film gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al’umma.
KU KARANTA: Kannywood Da Nollywood Sun Bani Dukkan Goyon Baya — Daraktan Shirin Mai Martaba
Abba El-mustapha ya ce an dauki matakin ne bayan dogon nazari domin kawo karshen korafe korafen da Hukumar take yawan karba dan kara inganta aiyukan Hukumar tare da masana’antar kannywood.
Sanarwar ta ce shirye-shiryen da abun ya shafa sun hada da:
1. Dakin Amarya
2. Mashahuri
3. Gidan Sarauta
4. Wasiyya
5. Tawakkaltu
6. Mijina
7. Wani Zamani
8. Labarina
9. Mallaka
10. Kudin Ruwa
11. Boka Ko Malam
12. Wa yasan Gobe
13. Rana Dubu
14. Manyan Mata
15. Fatake
16. Gwarwashi
17. Jamilun Jiddan
18. Shahadar Nabila
19. Dadin Kowa
20. Tabarma
21. Kishiyata
22. Rigar Aro
Sanarwar ta kara da cewa doka ce ta bawa hukumar damar tace duk wani film tare da lura da aiyukan ‘yan masana’antar kannywood matsawar suna da rejista da hukumar a ko ina suke, A saboda haka ana shawartar masu daukar nauyin wannan fina-finai da su tabbatar da sunbi dokar ta dakatarwa tare da tsayar da saka wannan fina-finai a gidajen TV ko kafar internet.
Haka kuma ana sanardasu cewa su miko fina-finansu ga Hukumar domin tantance su tare da basu shaidar inganci ta tacewa nanda sati daya mai zuwa wato daga Litinin, 19 ga watan Mayu, 2025 zuwa 25 ga Mayu, 2025 domin gujewa fushin doka.
A karshe Hukumar ta nemi hadinkan dukkannin gidajen TV da Hukumar dake lura da kafafen yada labaran ta Radio da Talabijin ta kasa wato NBC kan su cigaba da taimakawa Hukumarsa domin samun nasarar abinda ta saka a gaba da cigaban Jihar Kano da masana’antar kannywood.