• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

RATTAWU Ta Goyi Bayan Dakatar Da Shirye-shiryen Siyasa Kai-Tsaye a Kano

BySani Magaji Garko

May 19, 2025

Kungiyar ma’ikatan Radio da Talbijin da Dakunan Wasannin kwaikwayo ta kasa reshen jihar Kano RATTAWU ta jaddada goyon bayan ta ga matakin da shugabanni kafafen yada labarai a Kano suka dauka na dakaratar da shirye-shiryen siyasa kai-tsaye.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in hulda da jama’a ta kungiyar Hajiya Samira Hassan ta fitar tare da rabawa manema labarai a madadin Shugaban Kungiyar, Comrade Babangida Mamuda Biyamusu.

Sanarwar ta ce daukar matakin zai haifar da kyakkyawan sakamako wajen tsaftace kalamai a tsakanin masu shiga kafafen yada labarai Musamman shirye-shiryen siyasa.

KU KARANTA: Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Shirin Labarina, Dadin Kowa, Da Wasu Guda 20

Sanarwar tana yabawa kwamashinan yada labarai da harkokin cikin gida na Jihar Kano comrade lbrahim Abdullahi Waiya bisa amincewa da matakin da shugabanni suka dauka.

A wani cigaban ku, Shugabancin kungiyar ta RATTAWU reshen jihar Kano karkashin jagorancin kwamared Babangida Mamuda Biyamusu ta bayyana goyon bayan ta da matakin da hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta Dauka na dakatar da “Kauyawa Day” da “Yan mata keyi na nuna rashin Da’a a yayin Bukukuwa da matakin dakatar da kallon wasu fina-finai da hukumar ta yi.

Sanarwar tace matakin zai taimakawa wajen kawo tsaftar a Dabi’un al’umma
musamman yara mata domin samun al’umma ta gari.

Biyamusu ya yabawa shugaban hukumar Abba El-Mustapha bisa daukar matakin wanda ya ce zai taimaka wajen tsaftace harkokin fim da ma kare addini da al’adun al’ummar jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *