• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Hukumar Kare Hakkin Mai Siye Da Siyarwa Ta Kama Lalatattun Kaya Na Sama Da Miliyan 400 a Kano

BySani Magaji Garko

May 25, 2025

DAGA: IBRAHIM AMINU RIMIN KEBE, KANO

Hukumar kare hakkin mai siye da amfanin kayayyaki ta jihar Kano ta kama kaya na sama da kudi na naira miliyan dari hudu (400,000,000.00) wadanda wa’adin su ya kare a kasuwar Singa a jihar Kano.

Babban sakataran zartawar na hukumar Alhaji Zangina Jafaru ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai domin bayan nasarorin da hukumar tayi a yan kwanakin nan.

Jafaru ya kara da cewa, hukumar ta samu nasarar kama kayayyakin ne biyo bayan aiki tukuru da jami’an hukumar ta kare hakkin mai siye da amfanin kayayyaki ta jihar Kano suke yin na gudunar da sintirin a daukacin kasuwannin jihar nan domin ganin sun dakile dukkkanin wani gurbatttun kayayyakin da ake kokarin siyarwa da al’umma.

KU KARANTA: An Kashe Wani Mutum Saboda Ya Je Zance Wajen Budurwarsa a Kano

Ya ce daga cikin kayayyakin da hukumar ta kama a cikin kasuwar ta Singa wadanda wa’adin su ya kare sun hadar da Biskit katan 21 da kayan shafe shafe katan 21 da fulawa buhu 140 wanda cewar hakan babban nasara ce a gare su.

Zingina Jafaru yana mai bayyana cewa, wannan bashi ne karon farko ba da suke kama gurbatattun kayayyakin a cikin kasuwar ta Singa ba, domin ko a baya bayan nan sai da suka kama wasu lemukan sha wadanda wa’adin su ya kare.

Babban sakataran ya sake bayyana cewa, sun samu nasarar kama dakatar da wani kamfanin yin maganin sauro wanda bai inganta ba a yankin Dakata a karamar hukumar Nassarawa da ke Kano.

Daga bisani, Jafaru yayi kira ga al’ummar jihar ta Kano da su ci gaba da baiwa hukumar tasu dukkanin hadin kan da suke da bukata wajen basu rahotanni sirri domin dakile duk wani kaya da ake zargin ka iya cutar da al’ummar jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *