DAGA: NURA GARBA JIBRIN, KANO
Akalla mutane 20 ake tunanin sun mutu wanda suka Wakilci Jihar Kano a gasar wasanni ta kasa sakamakon hatsarin mota da su kayi a garin Chiromawa na karamar hukumar Garun-Malam a nan Kano.
Wasu bayanai da biyoyi da jaridar GLOBAL TRACKER ta samu sun ce motar mallakin hukumar Wasannin ta Jihar Kano ta yi Hatsarin ne kilomita 50 kafin shigowa Jihar Kano bayan sun dawo daga gasar Karo na 22 da aka gudanar a jihar Ogun.
Hatsarin ya rutsa da Yan Jaridu da jami’an lafiya da Yan wasa da kuma wakilan hukumar Wasannin ta Jihar Kano.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Abdulsamad Rabi’u, daya daga cikin jami’an lafiya na yan wasan.
Akwai karin bayani…..