• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Gwamnatin Kano Ta Ba Da Hutun Babbar Sallah

BySani Magaji Garko

Jun 2, 2025

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da umarni ga dukkan makarantun Firamare da na Sakandare a fadin jihar da su tafi hutun Babbar Sallah daga ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025 zuwa Lahadi, 15 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban makarantu kwana, sannan daga ranar Laraba 4 ga Yuni, 2025 zuwa Litinin 16 ga Yuni, 2025 ga ɗaliban jeka ka dawo.

Ma’aikatar Ilimi ta bakin Balarabe Abdullahi Kiru, daraktan yada labarai da wayar da kan jama’a ya sanya wa hannu ta bayyana cewa iyaye da masu kula da ɗaliban makarantun kwana su je su ɗauki ‘ya’yansu da sassafe a ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025.

Sanarwar ta ambato Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Dakta Ali Haruna Makoda yana kira ga iyaye da masu kula da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun dawo makaranta a ranar da aka tsara, tare da gode musu bisa goyon baya da hadin kai da suke bai wa ma’aikatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *