• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Kungiyar RATTAWU Ta Mika Ta’aziyyar Rasuwar Yan Wasan Kano 22

BySani Magaji Garko

Jun 2, 2025

Kungiyar ma’aikatan Radio, Talbijin da Dakunan Wasannin ta kasa reshen jihar Kano RATTAWU ta bayyana kudawar ta da rasuwar mutane 22 da suka kasance wasu daga cikin “yan tawagar wasan guje guje da tsalle tsalle na jihar Kano a hanyar su na dawowa gida daga garin Abekuta na Jihar Ogun.

Idan za’a iya tunawa dai a ranar Asabar din da ta gabata ne Yan asalin Jihar Kano wanda suka halarci gasar wasannin mota Jiki ta kasa da aka kammala a jihar Ogun su ka yi mummunan Hatsari a garin ciromawa na karamar hukumar Garun-malam wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 22 daga cikin 35 da suke a babbar motar daukar Yan wasa mallakin hukumar Wasannin ta Jihar Kano.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar reshen jihar Kano Comrade Babangida Mamuda Biyamusu ya fitar wacce ya aikowa da GLOBAL TRACKER.

KU KARANTA: DA DUMI-DUMI: Mutane 20 Sun Rasu Da Suka Wakilci Kano a Gasar Wasanni Ta Kasa

Sanarwar ta baiyyana matasan a matsayin zakakurai kuma “yan
kishin jihar Kano wanda tarihin Kano musamman a bangaren Wasannin ba zai taba mantawa dasu ba.

Comrade Biyamusu ya baiyyana cewa daukacin ‘ya’yan kungiyar ta RATTAWU sun nuna jimamin su da babban rashin tare da addu’ar Allah ya gafar ta musu yasa aljannatul Firdausi ce makomar su ya kuma baiwa iyalan su hakurin jure rashin ya kuma tashi kafadun wadanda suka jikkata.

Sanarwar ta aike da sakon ta’aziyya ga Gwamnan Kano da Mai martaba sarkin Kano da ma’aikatar matasa da wasanni dama al’umma jihar Kano baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *