• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Haramta Hawan Babbar Sallah

BySani Magaji Garko

Jun 3, 2025

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da haramta hawan Sallah a fadin jihar Kano.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, kakakin rundunar Yan Sandan Jihar Kano ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Sanarwar ta ce daukar matakin ya biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu da wasu mutane ke kokarin shirya tada-zaune-tsaye.

KU KARANTA: Zargin Karya Dokar Hawan Sallah: Rundunar Yan Sandan Kano Ta Gayyaci Sarki Sanusi

Sanarwar ta umarci masallata da zasu je sallar idi da su guji daukar muggan makamai ko Hawan dokuna don yin Kilisa ko gudu da motoci ko yin wani abu da zai iya kawo barazana ga zaman lafiya.

Sanarwar ta bukaci al’ummar jihar musamman iyaye da su ja kunnen ‘ya’yan su don kaucewa aka dukkan wasu laifuka a lokacin da bayan Sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *