DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO
Kungiyar masu Dillancin filaye ta jihar Kano KPADA ta gudanar da taron wayar da kai ga ‘ya’yan ta domin kara tsaftace harkar da kuma samar da cikakken hadin kai a tsakanin yayan kungiya da kuma kara tsaftace harkar siye da siyar da filaye da bada hayar gidaje a fadin jihar Kano.
Shugaban kungiyar na jihar Kano Alhaji Isah Jibril Isah wanda aka fi sani da “Kaci-kasa” shine ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce a yanzu kungiyar KPADA tana da kyakkyawar Alaka da gwamnati a matakai daban daban wanda hakan zai taimaka wajen kawo sabbin tsare tsare da zasu taimakawa wajen kauda bata gari dake cikin harkar da kuma bunkasa tattalin arzikin alumma jihar Kano ta fannin samar da ingantaccen mahalli.
KU KARANTA: Rundunar Yan Sandan Kano Ta Haramta Hawan Babbar Sallah
Shima a nasa jawabin, shugaban KPADA reshen karamar hukumar Gwale Alhaji Sani Jakara ya ce sun gudanar da taron bitar ne domin kara wayar da kai domin su kara fahimtar yadda zasu gudanar da sana’arsa kamar yadda doka ta tanada.
Da yake jawabi daya daga cikin shugabannin kungiyar a matakin jihar Kano Alhaji Bashir Tabarakalah ya bukaci masu gudanar da sana’a dasu sanya tsoran Allah da kuma gaskiya a yayin da suke gudanar da sana’arsu, wanda shine babban jigo na samu Nasara a duniya da lahira.