• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Trump Ya Haramtawa ‘Yan ƙasashen 12, Tsaurara Doka Ga Wasu 7 Wajen Shiga Amurka

BySani Magaji Garko

Jun 5, 2025

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya Haramtawa ‘Yan ƙasashen waje 12 Shiga kasarsa ta Amurka.

Haka kuma mista Trump ya bada umarnin tsaurara dokar shiga kasar ta Amurka ga wasu kasashen 7.

Cikin wani Bidiyo da GLOBAL TRACKER ta gani Trump ya ce Yan kasashen sun kasance barazanar tsaro ga Amurka.

KU KARANTA: DA DUMI-DUMI: Shugaban Amurka Trump Da Na Rasha Suna Tattaunawa Yanzu Haka.

Kasashe 12 da Trump ya haramtawa shiga Amurka sun hada da Afghanistan, Chad, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Haiti, Iran, Libya, Myanmar, Somalia, Sudan da kuma Yemen.

Sai kuma kasashe 7 da aka tsaurarawa dokokin shiga Washington wanda suka hada da Burundi, Cuba, Laos, Sierra Leone, Togo, Turkmenistan da kuma Venezuela.

“Harin ta’addancin da muka gani na baya-bayan nan a jihar Colorado dake nan Amurka ya nuna yadda mutanen wasu kasashen ke kasancewa barazana ga zaman lafiyar Amurka saboda yan wadannan kasashen suna zuwa Amurka kuma izinin zaman su ya kare amma sai su ki komawa kasashensu, saboda haka bana bukatar su kwata-kwata,” inji Trump

“Azamanin mulkina na farko, hana wasu mutane shigowa Amurka shine Irinsa na farko da yafi kowanne nasara, kuma ya bada matukar gudun mowa wajen hana aikata ta’addanci a cikin Amurka. KU sani ba za mu bari abin da ya faru a Nahiyar Turai ya faru a Amurka ba, idan kun ko a zamanin mulkina na farko na umarci Sakataren harkokin waje ya bamu shawara inda a wancan lokacin muka Hana mutane daga gurare da suke da hadari zuwa Amurka, saboda haka ne ya sa na dakatar da ‘yan wadannan kasashe daga shiga Amurka,” cewar Trump.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *