Wani lauya mai zaman kansa Barista Salisu Salisu Umar ya ce za su kai Sarki Muhammadu Sanusi II Kara Kotu bisa zarginsa da Daukar Nauyin Yan Daba da kuma razana mutane a lokacin bukukuwan Sallah a Kano.
Barista S.S. Umar ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a Kano ranar Laraba.
Ya ce abin takaici ne yadda shugabanni al’umma kamar Sarkin Kano ya gayyaci ko ya dauki Nauyin Yan Daba wanda suke barazana ga zaman lafiyar al’umma.
KU KARANTA: Sarkin Kano Na 15, Aminu Ado Ya Soke Dukkan Bukukuwan Sallah, Ya Ba Da Dalilai
“Tunda nake a rayuwa ta ban taba ganin taron Yan Daba masu mugun yawa da muggan makamai irin wannan lokacin ba, wannan abun takaici ne abin Allah-wadai, kuma munyi Allah-wadai da wannan Abu, kuma zamu dauki matakin shara’a domin ganin shara’a ta yi aikinta kuma Kotu ta hanu wannan abun, domin idan muna ganin yanzu ba wani abu bane, nan gaba sai yazo yafi karfin mu,” Inji Barista Umar.
“Mun shirya zamu tattara bayanai za kuma mu kai kara Kotu domin daukar matakin saboda wannan yunkurin wofuntar da zaman lafiyar Jihar Kano ne,” inji Lauyan.
Barista Umar ya kuma yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da ta dauki matakin ganin hakan Bata sake faruwa ba.
Idan za’a iya tunawa tun a shekarar 2024 rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta fara dakatar da hawan Sallah Bisa zargin wasu zasu fake da hawan wajen tayar da hankalin jama’a.
Ko a makon da ya gabata rundunar Yan Sandan ta sanar da hana hawan, kwanaki biyu bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana aniyar gudanar da hawan Sallah, to Amma bayan sanarwar Yan sanda fadar Sarkin Kanon itama ta fitar da sanarwar dakatar da gudanar da hawan sallar.
A wani cigaban labarin kuma, Barista Salisu Salisu Umar ya jajantawa Yan kasuwar Farm Center sakamakon ibtila’in gobara da ta afkawa wani bangare na kasuwar a Yan kwanakin nan.
Lauyan ya ce gobarar ta zo a dai-dai lokacin da mutane suke fama da masharsharar tattalin arziki da kuma karancin cikini a lokacin bukukuwan Sallah.
Ya kuma ya fatan Allah ya kare afkuwar gobarar a nan gaba, inda yayi fatan masu hanu da shuni da gwamnatoci su cigaba da tallafawa wadanda abun ya shafa.