• Fri. Jul 4th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Rasuwar Aminu Dantata Babban Rashi Ne Ga Harkokin Kasuwanci a Nigeriya — Shugaban Kamfanonin GERAWA

BySani Magaji Garko

Jun 29, 2025

Shugaban rukunin kamfanin Gerawa Alhaji Dakta Ibrahim Muhammad Gerawa ya bayyana rasuwar babban dan kasuwa kuma mai tallafawa Al’umma Alhaji Aminu Alhassan Dantata a matsayin babban rashin ga harkokin Kasuwanci a fadin tarayyar kasar nan.

Gerawa ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya aikowa GLOBAL TRACKER.

Sanarwar wacce kwamared Babangida Mamuda Biyamusu, mataimaki na musamman akan harkokin yada labarai ga shugaban kamfanin ta ce marigayin ya rasu a lokacin da al’umma take kishirwar irin su la’akari da yadda suke tallafawa mabukata da masu karamin karfi.

KU KARANTA: Mutane 5 Sun Rasu, 15 Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Bom a Kano

Sanarwar ta yi kira ga attajirai a Nigeriya da su yi koyi da halin Alhaji Aminu Alhassan Dantata na tallafawa mabukata.

Ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da gwamnatin Jihar Kano da ma al’umma, inda yayi adduar Allah ya sa Aljanna ce makomarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *