Shugaban kasa Ahmed Tinubu ya tarbi gawar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari bayan isowar sa daga birnin Londan.
Tinubu ya tarbi gawar ne a filin jirgin na Umaru Musa Yar’aduwa da ke Katsina inda za a tafi da ita zuwa Daura domin yin sallah da kuma binnewa.
Idan za’a iya tunawa a ranar Lahadi, 13 ga watan Yulin 2025 ne Buhari ya rasu a birnin Landan na kasar Birtaniya bayan doguwar jinya.