Kasashen Duniya 25 yanzu haka na gudanar da taro Bogota, babban birnin kasar Colombia don tattauna yakin da kasar Isra’ila ta ke yi a Gaza.
Ana zargin Isra’ila da aikata kisan kiyashi, ko da yake wakiliya ta musamman ta majalisar dinkin Duniya a yankin Falasdinawa ta ce laifin ya wuce zargi.
Taron wanda kasashen China da Spain da Ireland ke jagoranta, ana sa ran zai dauki babban mataki gami da fitar da matsaya dangane da Kiran da Isra’ila ke yiwa Falasdinawa a Gaza da sauran guraren da yahudawa Yan kama guri zauna suka kwace.
KU KARANTA: Yakin Gaza: Spain Da Ireland Za Su Kakabawa Isra’ila Takunkumi
Kasashen sun hada da Algeria, Bangladesh, Bolivia, Brazil, Chile, China, Colombia, Cuba, Djibouti, Honduras, Indonesia, Ireland, Lebanon, Malaysia, Namibia, Nicaragua, Oman, Portugal, Spain, Qatar, Senegal, South Africa, Turkey, Saint Vincent and the Grenadines, Uruguay da Palestine.