An tabbatar da cewa Jita-Jitar da ake yadawa game da rasuwar shahararren mawakin nan Aminudden Ladan Abubakar wanda aka fi sani da Aminu Ala ba gaskiya ba ce.
Wasu Jita-Jita da jaridar GLOBAL TRACKER ta samu ta bakin wakilanta sun bayyana cewa Aminu Ala ya rasu.
To Amma, Jaridar GLOBAL TRACKER ta tuntubi makusantan mawakin inda suka tabbatar yana raye cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali da nutsuwa.
KU KARANTA: Rasuwar Aminu Dantata Babban Rashi Ne Ga Harkokin Kasuwanci a Nigeriya — Shugaban Kamfanonin GERAWA
“Na bunkici maganar rasuwar Aminu Ala da ka tambaya kuma an tabbatar mun yana raye cikin koshin lafiya,” inji Muktar Dahiru Rigacikum, Dan jarida kuma mai bibiyar wakokin Ala.
“Jita-Jita ce kawai ake yadawa irin ta mawaka da ‘yan film, Amma na gaya maka wannan labarin ba gaskiya ba ne,” Inji Dan jaridar.
Haka kuma, wakilin GLOBAL TRACKER ya tuntubi Tijjani Sarki wanda shine Sakataren mawakin inda ya karyata Jita-Jitar.
“Ko a jiya sai da ni da Aminu Ala muka ga wannan Jita-Jita a kafafen sada zumunta, kuma munyi ta yi dariya saboda yadda wasu mutanen ke yada labaran karya, yau wajen kwanaki Uku kenan ana yada wannan Jita-Jitar,” inji Tijjani Sarki.