• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Ayyukan Rage Talauci Yakamata Gwamnatoci Su Mayar Da Kai Ba Gine-gine Ba — SKY

BySani Magaji Garko

Jul 30, 2025

DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO

Fitaccen dan kasuwa a nan Kano Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ya bukaci gwamnatoci a matakai daban daban na kasar nan dasu maida hankali wajen gudanar da ayyukan da zasu rage talauci a tsakanin al’umma.

Dan kasuwar ya shawarci gwamnoni duba da irin manyan ayyuka da suka gudanar a shekaru biyun da suka gabata, a yanzu lokaci ne da yakamata dasu karkata wajan aiwatar da kananan ayyuka da zasu inganta rayuwar alumma kai tsaye, wanda hakan zai rage aikata kanana laifuka a tsakanin al’umma.

Kamal Yakubu Ali wanda shine mai magana da yawun Dan kasuwar, ya ambato SKY na bayyana hakan ne a yayin bikin rufe karatun littafin Ashfa wanda Malam Abdulkadir Shehu mai Anwar ya gabatar a unguwar Tudun Yola dake karamar hukumar Gwale.

KU KARANTA: Mutane 5 Sun Rasu, 15 Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Bom a Kano

Ya ce a halin yanzu mutane suna cikin halin matsi da talauci wanda yake hana su walwala, a don haka ya kamata gwamnati tayi tunanin samar da ayyukan da zasu inganta rayuwar alumma kai tsaye wanda zai rage musu radadin halin da suke ciki.

SKY ya bukaci gwamnonin Arewacin Nigeriya dasu ware wasu makudan kudade da zasu dunga tallafawa yan kasuwa da sauran masu gudanar da sana’o’i daban daban; domin karfafa musu gwaiwa wajen bunkasa kasuwancinsu.

Ya ce a wannan lokaci da yawa daga cikin yan kasuwa masu karamin karfi jarinsu ya karye, ya kamata gwamnatin Tarayya da gwamnoni jahohi musamman na Arewacin Nigeriya su fito da wasu hanyoyi da zasu tallafawa alummar su yadda za a rage talauci da fatara da samar da ingantacciyar Rayuwa da zaman lafiya a cikin al’umma.

Dan kasuwar ya shawarci gwamnatin jihohi dasu samarwa da mañoma Taki kyauta domin a halin yanzu manoma suna bukatar tallafi daga gwamnati domin basa iya sayan Taki sakamakon tsadar da yayi wanda hakan ne zai taimaka wajen kokarin da gwamnati take na samar da abinci a cikin farashi mai sauki .

Ya kuma bukace su dasu samar da Gidaje kanana a gurare daban daban, duba da cikonso da ake fama dashi a cikin gari wanda yana taimakawa wajan haifarda aikata kananan laifuka a a tsakanin matasa kuma idan akayi hakan ma aikata da sauran masu karamin karfi zasu amfana da wannan aiki.

Taron ya samu halartar alumma da dama da suka hadar da limamai da suka hadar da hakimin kauran Namoda a jihar Zamfara da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *