Fitaccen tsohon jami’in Sojan Nigeriya Kanal Daudu Suleiman ya rasu.
Umar Daudu Suleiman, Daya daga cikin ‘ya’yan Marigayin ne ya tabbatar da rasuwar mahaifi nasu.
Kanal daudu Sulaiman tsohon Sojan Nigeria ne da ya ba da gagarumar gudunmawa wajen Hadin Kan Nigeriya.
KU KARANTA: Muna Fatan Zaka Inganta Samar Da Tallafin Karatu A Kano — Tsofaffun Daliban Jami’ar Northwest
An haifi Marigayin a garin Bebeji dake jihar Kano a ranar 17 Disambar 1942.
Ya rasu ne bayan ya yi fama da jinya a kasar masar.
Ya rasu ya bar ‘ya’yan 8 da jikoki da dama.
Idan za’a iya tunawa jaridar GLOBAL TRACKER ta rawaito muku yadda Marigayin Kanal Daudu Suleiman da sauran abokansa sukayi saukar Al’qur’ani mai girma a wani masallaci dake unguwar Hotoron Kudu kan titin Kanar Daudu (wani titi da aka saka sunan Marigayin domin tuna irin gudun mowar da ya bayar).
Nan gana za a sanar da lokacin da za’a yi jana’izarsa.