Kasar China ta bada da umarnin dakatar da siyan na’urar nadar bayanai wato “Chips wacce kamfanin “Nvidia” yake samarwa.
China ta dauki matakin ne a cewar mahukata don fargabar tsaro ko satar bayanai da kamfani da ke da shalkwata a birnin California na kasar Amurka ka iya yi kan harkokin tsaron Sin.
KU KARANTA: DA DUMI-DUMI: Trump Zai Sake Karawa China Haraji Zuwa Kashi 125
Wannan na zuwa ne bayan da kamfanin ya sanya hanu a yarjejeniyar bawa Amurka kaso 15 cikin 100 na ribar da ya samu a kayayyakin da ya siyar a China.
Amma rahotanni sun ce kamfanin ya sanya hanu a kan yarjejeniyar ne domin Amurka ta bashi lasisin siyar da kaya a dukkan kasuwannin Amurka da ma na kasashen Duniya.