Jam’iyyar APC mai ta nemi hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar tare da soke zaɓen cike gurbi da ke gudana yanzu haka a jihar Kano saboda “tashin hankali”.
Wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar ta ce ‘”‘yandaba sun tarwatsa kayayyakin zaɓe a ƙananan hukumomin Bagwai da Shanono da Gari”, inda ake gudanar da zaɓen ɗanmajalisar tarayya.
A cewarta: “Cigaba da kaɗa ƙuri’a a irin wannan yanayin na dabanci da tilasta wa masu zaɓe ya saɓa da tanadin dimokuraɗiyya na gudanar da sahihin zaɓe, kuma zai koyar da satar ƙuri’a da ba za a yarda da shi ba,” in ji sanarwar.
BBC Hausa ta rawaito cewa zuwa yanzu ba a kai ga samun sakamakon zaɓen a hukumance ba.