DAGA: YAHAYA SADISU ALKASIM, ASABA
Hukumar wasannin ta kasa ta tabbatar da cewa ‘Yan wasa da masu horar da su 6,382 zasu halarci gasar ajin matasa ta kasa karo ta 9 da za’ayi a Asaba Babban birnin jihar Delta.
A cewar hukumar wasannin ta Kasa tace hakan ya biyo bayan kammala yin rijista da akayi na jahohi 36 harda birnin tarayya Abuja.
Hukumar tace samun karuwar masu halartar gasar ta ajin matasa ta kasa ya biyo bayan yadda gasar take Kara bunkasa tare da samar da kwararrun matasan ‘yan wasa.
KU KARANTA: Hukumar Zakka Da Hubusi Ta Ziyarci Da Tallafawa ‘Yan Wasan Kano Da Sukayi Hatsari
‘Yan wasa 4,961 da masu horar dasu 386 da manajoji su 400 da suka fito daga jihohin kasar nan daban daban.
Wasannin 37 za’a fafata a kansu Wanda suka hada da wasan kwallon kafa da kwallon Raga da kwallon Dana kwando kwallon yashi da kwallon zari Ruga da sauransu daga cikin wasanni 9 da za’ayi na kungiyoyi.
Da kuma wasannin da yake kunsar mutane bibiyu ko mutun guda Wanda suka hada da tsaren gudu da Nunkaya da kokawa ta zamani da gargajiya da tseran Keke da jefa Abu Mai nauyin da Dana da dambin zamani.
Jihar Delta wadda itace a Kan gaba wajan zama ta daya, a wannan karon zata iya fuskantar kalubale a wajen jihohi irin su Ogun da Lagos da Rivers da kuma Edo.
Hukumar wasannin ta kasa ta bayyana cewa gasar ba anayi ne kawai don samun lambobin zinare ko azurfa ko tagulla ba Yana Samar da hadankan kasa tare da bawa matasa dama su nuna hazakarsu.
Shugabannin gudanar da gasar sun bayyana cewa wannan karon zai Sha Babban da gasar da akayi a baya a yayin da ake sa ran masu neman ‘yan wasa da masu horarwa tare da masu gudanarwa ana sa ran zasu kalli wasannin yadda ya kamata domin zakulo yanwasa da zasu iya wakiltar Najeriya nan gaba.
A yayin da zaa tantance yanwasa a yau Alhamis a gobe 29 ga watan Agusta zaa Bude gasar.