• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

KANO: Kungiyar RAAF Ta Mabiya Shi’a Ta Nemi a Saka Ta Cikin Mukabalar Da Za’ayi Da Malam Lawan Triumph 

BySani Magaji Garko

Oct 2, 2025

DAGA: BUHARI ALI ABDULLAHI, KANO

Kungiyar Rasulul A’azam Foundation (RAAF), wacce ta ƙunshi mabiya Ahlul Baiti na gidan Manzon Allah (S.A.W.) a Kano, ta kai ziyara ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, inda ta gabatar da muhimman korafe-korafe da kuma buƙatu dangane da shirin mukabalar da Majalisar Shura ta Jihar Kano za ta shirya da Malam Lawan Abubakar Triumph.

A yayin ziyarar, Shugaban ɓangaren Ta’aliki na kungiyar, Sheikh Bashir Lawan Kano, ya bayyana cewa RAAF na neman a saka ta cikin mahalarta mukabalar, kasancewar tana da tasiri da muhimmiyar rawa wajen isar da saƙon addini a jihar Kano.

Sheikh Bashir ya yi ƙorafi kan yadda ake maida mabiya Shi’a saniyar ware a harkokin gudanar da mulki da shari’ar addini a jihar, yana mai cewa hakan ba zai taimaka wajen gina zaman lafiya da haɗin kai ba.

KU KARANTA: CSADI Ta Tallafawa Mata Masu Juna Biyu Da Yara 400 Da Abinci Mai Gina Jiki a Kano

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da hukunta Malam Lawan matukar aka tabbatar da zarge-zargen da ake yi masa, tare da roƙon a bar kotu ta ci gaba da gudanar da shari’ar da ake yi wa Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ba tare da katsalandan daga ɓangarorin siyasa ko gwamnati ba.

Bugu da ƙari, shugaban kungiyar ya zargi tsohuwar gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje da nuna bangaranci tsakanin kungiyoyin addini a jihar, yana mai cewa hakan ne ya jefa al’amuran addini cikin rashin daidaito.

Sheikh Bashir Lawan ya kuma jaddada cewa mabiya Shi’a sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da gwamnatin jihar Kano a zaben da ya gabata, don haka su ma na da hakkin a mutunta su da kuma ba su gurbi a manyan lamurra na addini da siyasa.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnatin Kano da ta tabbatar da gaskiya da adalci a tsakanin dukkan mazahabobi, domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *