• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

KANO: CSADI Ta Rabawa Mata Masu Juna Biyu Da Yara 300 Abinci Mai Gina Jiki a Bebeji

BySani Magaji Garko

Oct 17, 2025

A kokarinta na yaki da cutar Tamowa wacce ke baraza ga lafiyar Mata da kananan yara musamman a yankunan karkara, kungiyar tallafawa Marayu da masu karamin karfi CSADI ta rabawa mata da kananan Yara su 300 garin Bul-Bul a garuruwa uku na a karamar hukumar Bebeji dake Jihar Kano.

Garin Bul-Bul dai wanda ake hadawa da Alkama da Gyada da Waken-soya da sauran sinadarai yana kara karfin garkuwar jikin Dan Adam da Kara Yawan ruwan Nono ga mata masu shayarwa da sauran amfaninsa ga mata da kananan yara, kuma an raba guda 600 a garuruwa da suka hada da Tariwa da Bebeji da kuma kauyen Durmawa cikin mazabar Kofa dukka a karamar hukumar ta Bebeji.

Shugabar kungiyar Hajiya Zainab Ahmad Suleiman MFR, JP, wacce ita ce ta jagoranci rabon ta ce garin na Bul-Bul wanda hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta amince da ingancin sa, kuma yana taka muhimmiyar rawa a kula da lafiyar al’umma.

KU KARANTA: CSADI Ta Tallafawa Mata, Yara Sama Da 600 Da Abinci Mai Gina Jiki, Ta Horar Da Su a Kano

“Na dauki gabarar tallafawa matan yankin ne saboda bukatar da ake da ita na abinci mai gina jiki, idan ka shiga yankunan zaka ga yara masu cutar yunwa, mafi yawancinsu Manoma ne, shi yasa muke basu wannan hadi, mu wayar musu da kai yadda ake hadawa da kuma muhimmancin hada shi don kula da lafiya,” inji Zainab Suleiman.

Shugabar CSADI Zainab Suleiman MFR JP da Tariwa, Alhaji Yawale Yahaya lokacin da kungiyar ta ziyarci garin Tariwa.

A jawabinsa, Dagacin garin Tariwa, Alhaji Yawale Yahaya ya bayyana farin cikinsa dangane da ziyarar wacce ya bayyana a matsayin mai matukar muhimmanci ga al’ummar yankin.

“Dangane da wannan tallafin, munyi farin ciki sosai, kuma munga yadda garin yake bada gudun mowar kula da lafiyar Mata da yaranmu, saboda haka muna fatan zata cigaba don kula da lafiyar al’ummar mu,” inji Dagacin.

Musa Muhammad Durmawa, shine Dagacin garin Durmawa cikin karamar hukumar Bebeji ya ce tallafin ya zo dai-dai lokacin da ake bukatar sa la’akari da garin na Bul-Bul yana da matukar amfani ga lafiyar Mata da kananan yara.

Wani bangare na mata lokacin da ake musu jawabinsa muhimmancin kula da lafiyar su da ta jariransu.

“Muna marhabun da wannan tallafi da wannan kungiya CSADI take kawowa al’ummar Durmawa, ko yanzu da kake gani ga mata da yara sun cika kofar gida na, wannan abun muna farin ciki da hakan, muna kuma fatan zai cigaba da kawo mana wadannan abubuwan alkhairi,” inji Dagacin.

Daya daga cikin Dattawan yankin Ashiru Garba ya ce kasancewar a baya sai sun kashe kudi a tafiye-tafiyen zuwa gurare masu nisa kafin siyo wadannan sinadarai, abin farin ciki ne a yanzu ake kawo musu har gida kuma Kyauta.

Garba ya kuma yi Alkawarin cigaba da bada gudun mowa don wayar da kan jama’a game da muhimmancin hadawa gami da sarrafa garin don kula da lafiyar al’ummar yankin.

A wani cigaban labarin kuma kungiyar ta gudanar da gwajin cuta mai karya garkuwar jikin Dan Adam a yankunan da aka ziyarta.

A dukkan gwaje-gwajen da akayi ba Sami ko mutum Daya Mai cutar ba lamarin da ke alamta Cigaban da aka samu a yaki da cutar HIV/AIDs a fadin Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *