Wani jigo a kungiyar Kwankwasiyya kuma tsohon mai baiwa gwamnan Kano shawara Alhaji Mustapha Hamza Buhari Bakwana ya bayyana tsohon gwamnan jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwakwaso a matsayin jagora mai hangen nesa kuma jigo a siyasar arewacin Najeriya wanda burinsa a koda yaushe shine ya bunkasa yankin Arewacin Nigeriya dama kasa baki daya.
Bakwana ya bayyana hakan ne a cikin sakon zagayowar ranar haihuwar Jagora Kwankwaso wanda ya cika shekaru 69 da haihuwa a ranar Talatan nan.
A cewar Bakwana, Kwankwaso wanda a halin yanzu shi ne jagoran jam’iyar NNPP kuma dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023 a jam’iyyar NNPP jajirtacce ne da ke ba da gudun mawa ga ci gaban kasa musamman ta fuskar ilimi da kiwon lafiya wanda ya canza rayuwar marasa adadi a jihar Kano da Najeriya baki daya.
READ ALSO: KANO: CSADI Ta Rabawa Mata Masu Juna Biyu Da Yara 300 Abinci Mai Gina Jiki a Bebeji
“A yau, muna karrama shugaban da yake da hangen nesa wanda burinsa shine cigaban al’umma da daukar matakin cigaban na kasa da shi. Kamar yadda muka shaida wannan rana mai cike da tarihi, Allah ya sa shekara mai zuwa ta cika domin cimma manufar mu, ta jawo al’ummarmu zuwa ga mafi kyawu a tarihi,” in ji Bakwana.
Daga karshe ya yi addu’ar Allah ya karawa tsohon gwamnan lafiya, ya kara masa lafiya, ya kuma kara masa nasara, yana mai bayyana fatan ganin shugabancin Kwankwaso a kasa zai ci gaba da zaburar da al’umma.
“Muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki da Ya baiwa jagoranmu Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso tsawon rai, arziki, kuma shiriyar Ubangiji,” inji shi.
Haka kuma, Bakwana ya bayyana kwarin gwiwar cewa salon jagorancin gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf zai bunkasa Kano zuwa babban birni mafi girma a kasar nan.
Mustapha wanda ya gamsu da ayyukan samar da ababen more rayuwa da ci gaban da gwamnatin jihar Kano ke aiwatarwa a halin yanzu, inda ya ce tabbas zai sauya fasalin jihar baki daya zuwa mafi kyawu a tarihi.