• Wed. Dec 10th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Hadin Gwiwar Sojojin Nijeriya da Faransa: Ma’anar Ziyarar Janar Charpy zuwa NDA Kaduna

BySani Magaji Garko

Nov 6, 2025

DAGA: SENATOR IROEGBU

Ziyarar da Laftanar Janar Emmanuel Charpy, kwamandan runduna ta musamman ta kasar Faransa wato (École Spéciale Militaire de Saint-Cyr (ESM) ta Faransa, ya kai Kwalejin Horar da Sojoji ta Nijeriya (NDA) da ke Kaduna, ta zama wata ziyara mai muhimmanci a huldar diflomasiyya tsakanin bangarorin biyu. Ta za wata hanyar kulla alaka mai ma’ana d zurfi ga tsaron ƙasa, haɗin kai da matsayin Nijeriya a fagen soja na duniya.

A dai-dai lokacin da ‘yan Siyasa ke gaggawar siyasantar da hulɗa tsakanin ƙasashe, ya zama wajibi a fahimci irin wannan ziyara a matsayin girmamawa da haɗin kai, ba nuna rauni ko dogaro ba. Wannan haɗin gwiwa tana nuni da ƙarfin Nijeriya da kuma ikon ta na yin hulɗa da ƙasashen duniya cikin mutunci da ‘yanci.

Wasu suna ganin kowace hulɗa da ƙasashen Yamma tana nufin dogaro, amma hakan ba daidai ba ne. Gaskiyar ‘yanci ita ce ikon yin aiki tare da ƙasashe masu ƙarfi cikin daidaito ba tare da rasa ikon yanke shawara ta ƙashin kai ba.

KU KARANTA: Hatsari Jirgin ‘Air India: Mutum 1 Daga Cikin 242 Ya Tsira, Shugabanni Kasashen Duniya Sun Mika Ta’aziyyar su

Kwalejin Horar da sojoji da NDA ta shafe fiye da shekaru 60 tana ba da horo ga sojoji, ta samar da fiye da dalibai 20,000, ciki har da waɗanda suka fito daga ƙasashe 14. Wannan ya sa ƙasashen duniya, ciki har da Faransa, ke kallonta a matsayin cibiyar da ake mutuntawa a Duniya.

 

Ziyarar Janar Charpy ta nuna cewa Nijeriya ta cancanci a girmamata, ba wai ana taimaka mata ba.

A yankin Sahel, ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar sun katse hulɗa da Faransa amma suka faɗa ƙarƙashin tasirin sojojin kasar Rasha ta hannun kamfanin Wagner Group.

Sakamakon hakan ne ya se tsaro ya tabarbare, fararen hula suna ta mutuwa, kuma ƙasashen sun rasa cikakken iko. Wannan darasi ne da Nijeriya ba za ta maimaita ba.

Maimakon keɓewa, dabarar Nijeriya ita ce ta faɗaɗa haɗin kai da ƙasashe da dama don amfanin juna. Muna kewaye da ƙasashen da ke magana da Faransanci kamar Nijar, Chadi, Kamaru da Benin. Don haka, sanin harshen Faransanci da haɗin gwiwa da ESM abu ne mai muhimmanci wajen musayar bayanan tsaro da zaman lafiya a yankin.

Haɗin kan NDA da ESM zai ƙarfafa koyarwa, jagoranci da ilimin harshe, wanda zai taimaka wajen ƙara ingancin rundunar sojin Nijeriya. Wannan haɗin gwiwa ba na dogaro ba ne, na koyon juna ne inda dukkan ɓangarori za su amfana.

A yau, harkokin tsaro na Nijeriya ya kamata ya dogara ne kan abin da ke amfani wa ƙasa, ba kan tarihi ko matsin lamba daga kasashen waje ba. Idan wannan haɗin gwiwa zai ƙara kwarewa da inganci ga sojojinmu, to ya dace a marabce shi.

Gaskiyar kishin ƙasa ba ta cikin ƙin hulɗa da ƙasashen waje, tana cikin yin amfani da kowace dama da za ta ƙarfafa ƙasar. Hakan na nufin koyon abin da ya fi kyau daga wasu domin ƙara ƙarfafa kanmu.

Ziyarar Janar Charpy ta zama alamar haɗin kai, kwarewa da matsayin Nijeriya a duniya. Tana nuna ƙasa mai ‘yanci da mutunci wadda ke son yin aiki tare da sauran ƙasashe domin samun ci gaba.

Maslahar Nijeriya ce a Farko kuma a kan gaba, ba bukatar kasashen Gabas, Yammacin Duniya ba.

(Senator Iroegbu masani ne kan tsaro, siyasar ƙasashen duniya da ci gaban ƙasa.)

Email: senator.iroegbu@yahoo.co.u

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *